Aliko Dangote wanda ke bayyana haka ne wajen wani taron tattalin arziki da kuma halin da Kano ke ciki a karshen mako, ya ce ya zama wajibi a duba rayuwar matasa ta hanyar sama musu ayyukan dogara da kai, bunkasa ilimi da kuma wayar da kan al'umma.
Yayin taron wanda ya gudana a Jami'ar Bayero da ke garin na Kano, shugaban sashen nazarin kasuwanci na Jami'ar Farfesa Murtala Sagagi ya ce yanzu haka akwai matasa fiye da miliyan 4 da basu da aikin yi a fadin jihar.
Farfesa Sagagi wanda ya dora alhakin hakan kan matakin rufe kamfanoni fiye da 500 a jihar ta Kano wanda gwamnatocin Najeriya da suka gabata suka yi, ya ce ya zama wajibi a dauka matakan bunkasa bangaren noma don maye gurbin rashin masana'antun.
Hamshakin attajirin na Najeriya Aliko Dangote, ya bukaci gwamnatin Najeriya ta yi duba kan halin da ake ciki a jihar ta Kano don farfado da kamfanoni tare da bunakasa harkar Noma da galibin al'ummar jihar suka dogara da shi.